Jihohi 26 Na Najeriya Sun Dogara Da FAAC Wajen Biyan Albashi
Jihohi 26 Na Najeriya Sun Dogara Da FAAC Wajen Biyan Albashi
Umar Nusaiba Ibrahim
Akalla jihohi 26 daga cikin jihohi 34 da aka yi nazari a kansu ba su samu isasshen kuɗin shiga na cikin gida ba, wato IGR, da zai iya ɗaukar nauyin albashin ma’aikatansu a shekarar 2025. Wani rahoton BudgIT ya nuna cewa jihohin sun ci gaba da dogaro da kuɗaɗen da suke samu daga Asusun Tarayya, wato FAAC, duk da ƙarin kuɗin da suke samu a cikin gida.
Rahoton ya nuna cewa jihohin 26 sun tattara kusan naira tiriliyan 1.16 daga IGR, amma sun kashe kimanin naira tiriliyan 1.91 wajen biyan ma’aikata. Hakan ya haifar da gibin kusan naira biliyan 747. Jihohin da suka samu IGR da ya fi abin da suka kashe kan albashi su ne Lagos, Enugu, Ogun, Delta, Kaduna, Kwara, Abia da Anambra.
A tsakanin jihohin Arewa, Yobe ce ta fi fuskantar babban gibi, inda ta tattara naira biliyan 15.42 na IGR amma ta kashe naira biliyan 76.34 wajen albashi. Jigawa kuwa ta samu naira biliyan 35.27 na IGR, yayin da ta kashe naira biliyan 92.66 kan albashi. Haka kuma, Kano ta kasance cikin jihohin da kuɗin shigarta na cikin gida bai kai kuɗin da ta kashe wajen biyan ma’aikata ba.
Rahoton ya kuma bayyana cewa kuɗaɗen FAAC da jihohi suka samu sun ƙaru daga naira tiriliyan 3.43 a shekarar 2022 zuwa naira tiriliyan 11.38 a 2025, yayin da IGR ya ƙaru daga naira tiriliyan 1.57 zuwa naira tiriliyan 4.15. Duk da wannan ƙarin kuɗaɗe, dogaro da FAAC ya ƙaru, inda rabon FAAC daga cikin kuɗin shiga na jihohi ya tashi daga kashi 68.7 zuwa kashi 73.3 cikin ɗari.
Masana tattalin arziki sun ce ya kamata gwamnatocin jihohi su ƙara samar da hanyoyin samun kuɗaɗen shiga na cikin gida, jawo jarin ‘yan kasuwa da samar da ayyukan yi domin rage dogaro da rabon FAAC. Sun kuma yi kira da a rage kashe-kashen da ba su da muhimmanci, musamman yawan ma’aikata da masu riƙe da mukaman siyasa, domin tabbatar da ɗorewar tattalin arzikin jihohi.
#Nigeria #FAAC #IGR #StateGovernments #NigeriaEconomy #BudgIT #Jigawa #Kano #Yobe #Sokoto #Kaduna #Katsina #Kebbi #Bauchi #Gombe #Borno #Zamfara #Niger #Nasarawa #Plateau #Arewa #NexviewTV #RFIHausa #Arewa24 #ArewaRadio #BBCHausa

Comments
Post a Comment