🚨 KADUNA: AN SAMU JARIRIN DA AKA SACE, AN KAMA WATA MATA
🚨 KADUNA: AN SAMU JARIRIN DA AKA SACE, AN KAMA WATA MATA
Samira Ahmad Danketa
An samu wani sabon jariri da aka sace daga gidansu a Sabon Gari New Extension, Kaduna ta Kudu, bayan an gano shi a Unguwar Ma’azu.
Mahaifiyar jaririn, Amina, ta ce wata mata ce ta zo gidansu ranar Lahadi, inda ta gabatar da kanta a matsayin ‘yar uwa ta nesa ga mahaifin jaririn, sannan ta É—auki jaririn.
Mazauna yankin sun fara zargin wata mata da ta yi ikirarin cewa ta haihu, bayan sun ga jaririn tare da ita amma ta kasa shayar da shi. Daga baya Amina ta je wurin, inda ta gane jaririn nata ne.
An kai lamarin ofishin ‘yan sanda, inda aka mayar wa Amina da jaririnta. Rundunar ‘yan sandan Kaduna ta tabbatar da faruwar lamarin tare da kama wadda ake zargi domin ci gaba da bincike.
#Kaduna #Jariri #SatarJariri #NigeriaNews #KadunaNews #Police #BreakingNews #HausaNews
#bbchausa #arewaradio

Comments
Post a Comment