🚨 AN KASHE MUTANE 12 A HARIN ADAMAWA
🚨 AN KASHE MUTANE 12 A HARIN ADAMAWA
Samira Ahmad Danketa
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Nzangula da ke Guyaku Ward, Æ™aramar hukumar Gombi a jihar Adamawa, inda suka kashe mutane 12 tare da jikkata mutum 2.
Shugaban ƙaramar hukumar Gombi, Markus Ishaya, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce waɗanda suka jikkata suna samun kulawa a Cottage Hospital da ke Gombi.
Rahotanni sun ce maharan sun kuma yi garkuwa da wata mata, tare da kona cocin EYN, gidaje uku da kuma lalata shaguna biyu.
Wani mazaunin yankin ya ce ana ci gaba da neman wasu mutanen da suka bace bayan harin, yayin da wasu mazauna suka tabbatar da cewa ‘yan uwansu na cikin waÉ—anda aka kashe.
Hukumomi ba su fitar da cikakkiyar sanarwa a hukumance kan harin ba.
#Adamawa #Gombi #HarinAdamawa #BokoHaram #Tsaro #NigeriaNews #BreakingNews #LabaranHausa

Comments
Post a Comment