Majalisar Ƙasa Ta Ƙara Wa’adin Kasafin 2025 A Karo Na Hudu


 

Majalisar Ƙasa Ta Ƙara Wa’adin Kasafin 2025 A Karo Na Hudu


Umar Nusaiba Ibrahim 


Majalisar Ƙasa ta tsawaita wa’adin aiwatar da ɓangaren ayyukan raya ƙasa na kasafin kuɗin shekarar 2025 daga ranar 30 ga Satumba zuwa 31 ga Disamba 2026. Wannan shi ne karo na huɗu da aka ƙara wa’adin aiwatar da kasafin kuɗin ayyukan raya ƙasar na shekarar 2025.


A Majalisar Dattawa, Shugaban Masu Rinjaye, Opeyemi Bamidele, ya ce matakin ya zama dole domin bai wa ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnati isasshen lokaci don kammala ayyukan da aka ware musu kuɗaɗe. Ya bayyana cewa hanyoyin sayen kayayyaki, aiwatar da kwangiloli, biyan kuɗaɗen fara aiki da tantance ayyukan da aka kammala na iya jinkirta aiwatar da ayyukan.


Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya goyi bayan tsawaita wa’adin, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage yawaitar ayyukan gwamnati da ake bari ba a kammala su ba. Shi ma Shugaban Marasa Rinjaye, Abba Moro, ya amince da matakin, amma ya yi kira ga ‘yan majalisar da su guji mayar da batun wata dama ta zargin juna da siyasa.


A Majalisar Wakilai ma an amince da tsawaita wa’adin a karo na huɗu, bayan wata ƙuduri da Shugaban Masu Rinjaye, Julius Ihonvbere, ya gabatar. Wannan matakin zai bai wa ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya ƙarin watanni uku domin aiwatar da ayyukan da ke cikin kasafin 2025 tare da amfani da kuɗaɗen da aka ware musu.


Tun a watan Disamba na 2025 ne Majalisar Ƙasa ta fara tsawaita wa’adin kasafin, inda ta kai shi zuwa 31 ga Maris 2026, daga nan zuwa 30 ga Yuni, sannan zuwa 30 ga Satumba. Sai dai wani masanin tattalin arziƙi, Dr. Marcel Okeke, ya soki matakin, yana mai cewa yawan tsawaita wa’adin kasafin na iya kawo matsala ga tsarin kula da kuɗaɗen gwamnati tare da rage ingancin sa ido kan ayyukan da aka ware wa kuɗaɗen.


Wasu lauyoyi da masu fafutukar tabbatar da gaskiya ma sun nuna damuwa kan tasirin matakin ga tsarin kula da kuɗaɗen gwamnati. Lauya Udochukwu Onoh ya ce ya kamata a tabbatar da cewa an yi cikakken bayani kan kuɗaɗen da ba a kashe ba kafin shiga sabon zangon kasafi, yayin da Victoria Adaji da Friday Odeh suka yi gargadin cewa yawan tsawaita wa’adin na iya kawo ƙalubale ga tsarin sa ido da bin diddigin yadda ake kashe kuɗaɗen jama’a.



#NexViewTV #Nigeria #NationalAssembly #Budget2025 #KasafinKudi #MajalisarKasa #Arewa #ArewaNews #LabaranArewa #HausaNews #BBCHausa #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa #FreedomRadioKano #DailyTrust #TattalinArziki #GwamnatinNigeria #LabaranKasa

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

KANO BRIDE SENTENCED TO DEATH BY HANGING 9 DAYS AFTER WEDDING