Muhawarar Farashin Fetur: Makinde Ya Gabatar da Sabuwar Hanya
Muhawarar Farashin Fetur: Makinde Ya Gabatar da Sabuwar Hanya
Samira Ahmad Danketa
Gwamnan Jihar Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na APM, Seyi Makinde, ya ce Najeriya za ta iya samar da man fetur a farashi mai rahusa idan aka sauya tsarin farashi da samar da ɗanyen mai ga matatun cikin gida.
Makinde ya jaddada cewa ba ya goyon bayan komawa tsarin tallafin mai, yana mai cewa mafita ita ce a tabbatar da cewa ɗanyen man da Najeriya ke samarwa yana amfani ga ‘yan ƙasar kai tsaye, musamman ta hanyar matatun cikin gida.
Ya kuma yi kira da a samar da cikakken bayani kan yadda ake ƙayyade farashin man fetur, daga hako ɗanyen mai zuwa tacewa, sufuri, rarrabawa, haraji da ribar ‘yan kasuwa, domin ‘yan Najeriya su san abin da suke biya.
Gwamnan ya ce wannan shawara na cikin “Reset Nigeria Agenda” da yake gabatarwa, yayin da ake ci gaba da muhawara kan cire tallafin man fetur da yadda aka yi amfani da kuɗaɗen da aka samu daga hakan.
A gefe guda, Makinde ya ce jam’iyyarsa ta APM ba ta shiga takarar shugaban ƙasa ta 2027 domin cike gurbi kawai ba. Ya ce idan miliyoyin ‘yan Najeriya suka haɗa kai wajen neman kyakkyawar makoma, ba za a iya yin watsi da muryarsu da ƙarfinsu ba.
#SeyiMakinde #APM #FuelPrice #PetrolSubsidy #Nigeria #2027Election #ResetNigeria #NigeriaNews

Comments
Post a Comment