NANS Ta Gargadi Jami’o’i Kan Riƙe Kuɗaɗen Maido wa Dalibai Na NELFUND
NANS Ta Gargadi Jami’o’i Kan Riƙe Kuɗaɗen Maido wa Dalibai Na NELFUND
Umar Nusaiba Ibrahim
Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya ta Ƙasa (NANS), reshen Zone C, ta gargadi manyan makarantu da ke yankin Arewa ta Tsakiya da su gaggauta mayar wa ɗaliban da suka biya kuɗin makaranta kafin samun rancen NELFUND kuɗaɗensu, tana mai cewa ba za a amince da riƙe kuɗin ba bayan Asusun Ilimi na Ƙasa ya biya wa ɗaliban kuɗin makaranta.
NANS ta bayyana damuwa kan yadda wasu cibiyoyin ilimi ke jinkirta mayar da kuɗaɗen ga ɗaliban da abin ya shafa, duk da cewa NELFUND ta riga ta biya kuɗin karatunsu. Mai kula da NANS Zone C, Abiola Babatunde, ya ce hakan na ƙara wa ɗalibai matsin tattalin arziki kuma ya sabawa manufar shirin rancen ɗalibai na Gwamnatin Tarayya.
Ƙungiyar ta kuma yi Allah-wadai da wasu kuɗaɗen da take ganin sun yi yawa da kuma wasu haraji da cibiyoyin ilimi ke ɗora wa ɗalibai, musamman kuɗaɗen jinkirin biyan makaranta da wasu kudade da ba a bayyana su a fili ba. NANS ta bukaci makarantu da su sake duba tsarin kuɗaɗensu tare da tabbatar da cewa ɗalibai suna samun cikakken abin da suka biya kuɗi a kai, kamar ingantattun azuzuwa, dakunan gwaje-gwaje, masauki, kiwon lafiya, ruwa da wutar lantarki.
NANS Zone C ta ce NELFUND ma ta gudanar da bincike kan cibiyoyin ilimi kusan 34 da ake zargi da gazawa wajen mayar wa ɗalibai kuɗaɗen da suka cancanta, bayan samun korafe-korafe daga waɗanda abin ya shafa. Ƙungiyar ta buƙaci makarantu da ke Kwara, Benue, Niger, Kogi, Plateau, Nasarawa da Abuja su gaggauta warware matsalar tare da tabbatar da cewa duk wani kuɗi da ya dace a mayar wa ɗalibi an ba shi ba tare da wani tsaiko ba.
A wani ɓangare kuma, NANS ta yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara tsaurara matakan tsaro a jami’o’i da sauran manyan makarantu da garuruwan da suke kewaye da su. Haka kuma, ƙungiyar ta bai wa makarantun da ba su gudanar da zaɓen ƙungiyar ɗalibai ba wa’adin makonni biyu da su fara tare da kammala tsarin zaɓen, tana mai cewa za ta ɗauki matakan da ta kira na halal da tsarin mulki a kan duk makarantar da ta ƙi bin umarnin.
#NANS #NELFUND #StudentLoan #TertiaryEducation #NigeriaStudents #Education #StudentRefund #HigherEducation #NigeriaNews #NorthCentral #NexviewTV #HausaNews

Comments
Post a Comment