NAPTIP Ta Bukaci Al’ummomin Iyakokin Ogun Su Ƙara Yaƙi da Safarar Mutane
NAPTIP Ta Bukaci Al’ummomin Iyakokin Ogun Su Ƙara Yaƙi da Safarar Mutane
Daga Zamira Ahmad Nasidi
Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) ta buƙaci mazauna al’ummomin da ke kan iyakar Ogun State da su ƙara haɗa kai da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin yaƙi da safarar mutane da kuma cin zarafin bil’adama.
Hukumar ta kuma gargaɗi ’yan Najeriya da su yi taka-tsantsan da tayin neman aiki ta kafafen intanet da sauran alkawuran da ake yi masu da nufin yaudararsu, tana mai cewa safarar mutane ta sauya salo tare da ƙara ɗaukar sabbin hanyoyi kamar cin zarafin jima’i, satar gabobin jiki, sextortion da safarar yara.
Kwamandan NAPTIP na Ogun State, Bose Jimoh, ce ta yi wannan kira a ranar Juma’a yayin wani taron yini biyu na wayar da kan al’umma da tattaunawa kan safarar mutane da cin zarafin bil’adama da aka gudanar a Idiroko, Ƙaramar Hukumar Ipokia ta Ogun State.
An shirya taron ne tare da haɗin gwiwar International Centre for Migration Policy Development (ICMPD), inda shugabannin gargajiya da na addini, kwamitocin ci gaban al’umma, ƙungiyoyin matasa, ’yan kasuwa, ma’aikatan sufuri, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki suka halarta.
Jimoh ta ce manufar taron ita ce bai wa al’umma da masu ruwa da tsaki ilimin da ya dace domin su iya gano alamomin safarar mutane da kuma kai rahoton duk wani abin da ake zargi ga hukumomin da abin ya shafa.
Ta bayyana cewa Idiroko na da muhimmiyar rawa wajen yaƙi da safarar mutane saboda kasancewarsa ɗaya daga cikin manyan mashigar ƙasa da ƙasa da ake amfani da su wajen shigar da mutane da fitar da su daga ƙasar.
Kwamandan ta ƙara da cewa masu safarar mutane na ci gaba da sauya dabarunsu wajen yaudarar waɗanda suke hari, don haka ya zama wajibi al’umma su kasance cikin shiri tare da kai rahoton duk wani abin da ake zargi.
A nasa jawabin, Jami’in Ayyuka na ICMPD kuma mai kula da School Anti-Trafficking Education and Advocacy Project, Samuel Okoroji, ya ce an shirya taron ne domin wayar da kan mazauna al’ummomin kan iyakoki game da illolin safarar mutane da cin zarafin bil’adama.
Ya ce an zaɓi Idiroko ne musamman saboda wuraren kan iyaka na cikin wuraren da suka fi fuskantar barazanar safarar mutane, kasancewar su mashigar shiga da fita tsakanin ƙasashe.
Okoroji ya ce taron zai kuma ƙarfafa gwiwar al’umma wajen hana safarar mutane, kai rahoto, tura waɗanda abin ya shafa zuwa wuraren samun taimako, kama waɗanda ake zargi da kuma gurfanar da su a gaban kotu.
A ƙarshen taron, mahalarta 102 sun amince da ƙara yaƙi da safarar mutane ta hanyar ci gaba da wayar da kan jama’a a masallatai, coci-coci, makarantu, kasuwanni da sauran wuraren taruwar jama’a.
#NAPTIP #SafararMutane #HumanTrafficking #OgunState #Idiroko #Ipokia #NigeriaNews #LabaranNajeriya #AntiTrafficking #ViolenceAgainstPersons #ChildTrafficking #CommunityAwareness #BorderCommunities #Nigeria

Comments
Post a Comment