🇳🇬 NATIONAL ASSEMBLY TA DAKATAR DA ZIYARAR AFIRKA TA KUDU SABODA HARIN XENOPHOBIA


 

🇳🇬 NATIONAL ASSEMBLY TA DAKATAR DA ZIYARAR AFIRKA TA KUDU SABODA HARIN XENOPHOBIA


Daga Zamira Ahmad Nasidi 


Majalisar Dokokin Najeriya ta dakatar da dukkanin ziyarar aiki da wakilan Majalisar Dokokin Æ™asar ke kaiwa Afirka ta Kudu, tare da umartar ‘yan majalisa da jami’anta da su kaurace wa duk wani taron majalisa da hukumomin Afirka ta Kudu suka shirya ko suka dauki nauyi.


Matakin ya fara aiki nan take, kuma zai ci gaba da kasancewa a wurin har sai an ba da wata sabuwar sanarwa.


A cewar shugabancin Majalisar Dokokin Najeriya, matakin ya biyo bayan damuwa kan rahotannin hare-haren Æ™iyayya da ake zargin ana kai wa ‘yan Najeriya da sauran ‘yan Æ™asashen Afirka da ke zaune ko gudanar da harkokinsu a Afirka ta Kudu.


Rahotannin sun haÉ—a da kisan gilla, raunata mutane, tsoratarwa, lalata kadarori da tilasta wa wasu ‘yan Najeriya barin gidajensu da wuraren kasuwancinsu.


Dakatarwar ta shafi:


- Ziyarar aiki ta Majalisar Dokokin Najeriya.

- Kwamitocin majalisa da ‘yan majalisa.

- Jami’ai da ma’aikatan Majalisar.

- Taro, tarukan karawa juna sani da bitoci.

- Taron musayar kwarewa tsakanin majalisu.

- Sauran ayyukan majalisa da hukumomin Afirka ta Kudu suka shirya ko suka dauki nauyi.


Haka kuma, an bayyana cewa dokar kauracewar ta shafi halartar tarukan kai tsaye da kuma shiga ta kafafen intanet (virtual/online).


Shugabancin Majalisar ya ce abin da ya fi tayar musu da hankali shi ne rahotannin yadda wasu ‘yan Najeriya ke rasa rayukansu, samun raunuka ko kuma tilastawa barin kasuwanci, gidaje, jarinsu da sauran kadarorinsu sakamakon hare-haren da ake dangantawa da xenophobia.


Majalisar ta kuma bayyana cewa, duk da kiraye-kirayen da gwamnatin Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki suka yi ga hukumomin Afirka ta Kudu da su kara daukar matakan kare ‘yan Najeriya da sauran ‘yan kasashen waje tare da gurfanar da wadanda ke da hannu a hare-haren, har yanzu ana ci gaba da samun rahotannin irin wadannan abubuwa.


Ta kuma amince da kokarin da gwamnatin tarayya da sauran hukumomi ke yi wajen taimaka wa ‘yan Najeriya da abin ya shafa, ciki har da kokarin dawo da wasu ‘yan Najeriya daga Afirka ta Kudu.


Shugabancin Majalisar ya umarci Clerk of the National Assembly da ya isar da wannan kuduri ga majalisun biyu, kwamitoci, sassa da dukkan jami’ai da ma’aikata domin tabbatar da cikakken bin umarnin.


Sai dai Majalisar ta jaddada cewa matakin ba wai an dauke shi ne da nufin lalata kyakkyawar dangantakar tarihi, diflomasiyya da alakar jama’a tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu


#Nigeria #NationalAssembly #SouthAfrica #Xenophobia #NigeriansInSouthAfrica #NigeriaNews #SouthAfricaNews #Diplomacy #NigerianParliament #BreakingNews #LatestNews

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

KANO BRIDE SENTENCED TO DEATH BY HANGING 9 DAYS AFTER WEDDING