NECO Ta Fitar Da Sakamakon SSCE Na 2026


 


NECO Ta Fitar Da Sakamakon SSCE Na 2026


Umar Nusaiba Ibrahim 


Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sakandare ta Ƙasa, NECO, ta fitar da sakamakon jarabawar Senior School Certificate Examination (SSCE) ta shekarar 2026. Rajistara hukumar, Farfesa Dantani Wushishi, ce ta bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai.


A cewar hukumar, ɗalibai 1,378,048 ne suka yi rajistar jarabawar, yayin da 1,371,992 suka zauna domin rubuta jarabawar. Daga cikin waɗanda suka rubuta, ɗalibai 804,948, wato kashi 58.67 cikin 100, sun samu maki biyar ko sama da haka, ciki har da Turanci da Lissafi.


Hukumar ta kuma bayyana cewa ɗalibai 1,126,118, kwatankwacin kashi 84.70 cikin 100, sun samu maki biyar ko sama da haka ba tare da la’akari da samun Turanci da Lissafi ba.


Dangane da magudin jarabawa, NECO ta ce ɗalibai 1,496 ne aka samu da hannu a irin wannan laifi a shekarar 2026, idan aka kwatanta da 3,878 da aka samu a shekarar 2025. Hakan na nuna raguwar adadin masu magudin jarabawar da kashi 64.74 cikin 100.


Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Wushishi ya ce amfani da tsarin jarabawar kwamfuta, CBT, ya taimaka wajen rage yawan magudin jarabawa a jarabawar NECO. Ya kuma bayyana cewa hukumar ba ta da hannu a abin da ake kira “miracle centres”, yana mai cewa NECO makaranta guda ɗaya ce kawai take da ita.


Wushishi ya ce idan akwai cibiyoyin da ake kira “miracle centres”, to gwamnati ko masu zaman kansu ne suka kafa su, domin NECO na da ƙa’idojin da take bi kafin ta yi wa kowace cibiya rajista.


#NECO #NECO2026 #SSCE2026 #NECOResults #ExamResults #Education #Ilimi #NigeriaEducation #HausaNews #LabaranHausa #BBCHausa #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa #FreedomRadioKano #DailyTrust #PUNCH #Arewa #NigerianNews #NexViewTV #NexViewNews #LabaranYau #Nigeria #IliminNijeriya

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

KANO BRIDE SENTENCED TO DEATH BY HANGING 9 DAYS AFTER WEDDING