NNPCL Ta Bayyana Faduwar Yawan Hakar Mai A Yuli
NNPCL Ta Bayyana Faduwar Yawan Hakar Mai A Yuli
Umar Nusaiba Ibrahim
Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya bayyana cewa yawan danyen man fetur da condensate da Najeriya ta samar ya ragu zuwa ganga miliyan 1.68 a kowace rana a watan Yulin 2026.
Rahoton ayyukan kamfanin na watan Yuli ya nuna cewa adadin ya ragu daga ganga miliyan 1.73 a kowace rana a watan Mayu, zuwa miliyan 1.72 a watan Yuni, kafin ya kara faduwa zuwa miliyan 1.68 a watan Yuli.
NNPCL ya danganta raguwar da matsalolin aiki a wasu wuraren hakar mai, ciki har da lalacewar wasu kayan aiki, matsalolin bututun mai da kuma dakatarwar wasu cibiyoyin samar da mai. Kamfanin ya ce sayar da danyen mai da condensate ma ta ragu zuwa ganga miliyan 22.53 a Yuli daga miliyan 28.23 a watan Yuni.
A bangaren kudaden shiga kuwa, NNPCL ta ce ta samu Naira tiriliyan 3.09 a matsayin kudaden shiga tare da samun Naira biliyan 279 na ribar bayan haraji. Haka kuma, ta ce ta tura Naira tiriliyan 7.91 zuwa Asusun Tarayya tsakanin watan Janairu da Yuli 2026.
Kamfanin ya ce yana daukar matakan kara dawo da yawan samar da mai, ta hanyar inganta kula da kayayyakin aiki, rage lokutan da ake dakatar da aiki ba tare da shiri ba, da inganta hanyoyin fitar da mai. NNPCL ta kuma bayyana cewa samar da iskar gas ya kai biliyan 7.49 scf a kowace rana, yayin da sayar da iskar gas ya kai biliyan 4.6 scf a kowace rana
#NNPCL #NigeriaOil #CrudeOil #OilProduction #NigerianEconomy #Petroleum #NNPC #OilAndGas #NigeriaNews #NexviewTV #HausaNews

Comments
Post a Comment