Ranar Samun ’Yancin Kai: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana 1 Ga Oktoba A Matsayin Hutun Kasa
Ranar Samun ’Yancin Kai: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana 1 Ga Oktoba A Matsayin Hutun Kasa
Umar Nusaiba Ibrahim
Gwamnatin Tarayya ta ayyana Alhamis, 1 ga Oktoba, 2026, a matsayin ranar hutu ta ƙasa domin bikin cika shekaru 66 da samun ‘yancin kan Najeriya.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a madadin Gwamnatin Tarayya, inda ya taya ƴan Najeriya da ke cikin gida da ƙasashen waje murnar bikin cika shekaru 66 da samun ‘yancin kai.
Tunji-Ojo ya bayyana cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali su ne ginshiƙan ci gaban kowace ƙasa. Ya bukaci ƴan Najeriya da su yi koyi da kishin ƙasa da jajircewar waɗanda suka kafa Najeriya, tare da ba da gudummawa wajen gina ƙasar da al’ummarta da ‘ya’yansu za su yi alfahari da ita.
Ministan ya ce bambancin al’adu da harsuna da ake da su a Najeriya ya kamata a ɗauke su a matsayin ƙarfi, yana mai cewa haɗin kan ‘yan ƙasa da ƙudurin gina ƙasa mai ƙarfi za su taimaka wajen samar da makoma mai kyau.
Ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya, ta hanyar ajandar Renewed Hope, za ta ci gaba da kokarin samar da Najeriya mai inganci ga kowa, a matsayin girmamawa ga waɗanda suka sadaukar da rayukansu wajen tabbatar da ‘yancin ƙasar.
Tunji-Ojo ya yi kira ga ƴan Najeriya da su yi amfani da bikin ranar samun ‘yancin kai wajen nuna haɗin kai, kishin ƙasa, zaman lafiya, mutunta juna da kuma zaman tare cikin lumana.
#NexViewTV #IndependenceDay #NigeriaAt66 #October1 #Nigeria #Arewa #ArewaNews #LabaranArewa #HausaNews #BBCHausa #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa #FreedomRadioKano #DailyTrust #IndependenceDay2026 #LabaranKasa #LabaranDuniya

Comments
Post a Comment