RIGAR JULIÁN ÁLVAREZ TA ƁACE ƁAT A SHAGON ATLETICO MADRID SABODA RIGIMAR TRANSFER


 

RIGAR JULIÁN ÁLVAREZ TA ƁACE ƁAT A SHAGON ATLETICO MADRID SABODA RIGIMAR TRANSFER


 Wata gagarumar dambarwar wasanni ta ɓalle a yau Asabar, inda aka gano cewa babu ko riga guda ɗaya ta ɗan wasa Julián Álvarez da ake sayarwa a halin yanzu a cikin babban shagon kayan wasanni na Atletico Madrid da ke filin wasa na Metropolitano.


Wannan lamari ya faru ne bayan kammala kasuwar musayar ’yan wasa, inda majiyoyi suka tabbatar cewa da gangan aka janye rigar tasa mai lamba 19 daga kasuwa saboda halin da ya nuna.


Julián Álvarez ya matsa kaimi yana son barin Atletico Madrid domin komawa ƙungiyar Barcelona a lokacin kasuwar canjin ɗan wasa, lamarin da ya fusata shugabannin Atletico suka hana shi tafiya.


 Jin labarin cewa tauraron nasu yana son tafiya Barcelona ya sa magoya bayan Atletico fushi na fitar hankali. 


Wasu ma sun je har sansanin horarwa sun manna masa takarda mai rubutun “JUFIÁN FUERA” (Julián ya Fita).


Duk da cewa Álvarez yana da ragowar kwangila ta shekaru shida, janye rigarsa daga shago ya nuna a sarari

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

KANO BRIDE SENTENCED TO DEATH BY HANGING 9 DAYS AFTER WEDDING