SOKOTO: An Kashe Matashin Da Ya Caka Wa Malamin Addini Wuka Bayan Sallar Juma’a
SOKOTO: An Kashe Matashin Da Ya Caka Wa Malamin Addini Wuka Bayan Sallar Juma’a
Umar Nusaiba Ibrahim
An kashe wani matashi bayan zargin caka wa wani malamin addini, Malam Musa Lukwa, wuka jim kaɗan bayan kammala sallar Juma’a a wani masallaci da ke yankin Mabera a birnin Sokoto.
Rahotanni sun ce matashin, wanda aka bayyana da suna Mai Barewa, yana cikin masu ibada a sahun gaba kafin ya kai wa Malam Lukwa hari, inda ya caka masa wuka har sau biyu a wuya. Daga bisani, wasu daga cikin masu ibadar sun yi galaba a kansa tare da lakada masa duka har ya mutu.
An ce harin na da alaƙa da wata hujja da Malam Lukwa ya taɓa kawo wa a cikin wa’azinsa, inda ya ambaci wani Hadisi da wasu malaman addini masu alaƙa da Ɗariƙa suka ce ya ɓata wa iyayen Annabi Muhammad ﷺ rai. Bayan wannan batu, Mai Barewa ya zargi Malamin da kuma babban ɗalibinsa, Malam Murtala Assada, da yin abin da bai dace ba tare da yin barazanar kashe su.
Rahotanni sun ƙara da cewa Malamin da mabiyansa sun kai ƙarar barazanar ga ’yan sanda, lamarin da ya kai ga kama matashin tare da gurfanar da shi a gaban kotu. Kotun ta bayar da umarnin tsare shi a gidan gyaran hali na wani lokaci, yayin da shari’ar ke ci gaba. Haka kuma, kwanaki huɗu kafin harin na Juma’a, Malaman sun kai ƙorafi a rubuce zuwa gidan gwamnatin jihar Sokoto.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufa’i, ya tabbatar da faruwar harin, yana mai cewa Malam Lukwa na karɓar magani a Asibitin Kwararru na Sokoto. Ya ce wanda ake zargi da kai harin ya mutu bayan mabiyan Malamin sun lakada masa duka. Kakakin ya ƙara da cewa ba a kama wani mutum kan kisan ba, yayin da jami’an tsaro suka ɗauki matakan hana lamarin ƙara ta’azzara, tare da gudanar da bincike domin gano cikakken abin da ya faru da kuma duk wadanda ke da hannu.
#Sokoto #MalamMusaLukwa #JumaAt #Islam #NigeriaNews #SokotoNews #NexViewTV #ArewaNews #HausaNews #BreakingNews #ArewaRadio

Comments
Post a Comment