Tinubu Ya Hana Aikin “White Elephant”, Ya Gargadi Hukumar Raya Yankuna
Tinubu Ya Hana Aikin “White Elephant”, Ya Gargadi Hukumar Raya Yankuna
Umar Nusaiba Ibrahim
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gargadi hukumomin raya yankuna da su guji kashe kuɗaɗen gwamnati wajen aiwatar da ayyukan da ba su da ingantaccen tsari ko kuma waɗanda ba za su samar da amfani mai ma’ana ga al’umma ba.
Tinubu ya yi wannan gargaɗin ne a ranar Litinin, lokacin da aka buɗe taron farko na masu ruwa da tsaki kan ci gaban Arewa ta Tsakiya, wanda Hukumar Raya Yankin Arewa ta Tsakiya, NCDC, ta shirya a Abuja. Shugaban Ƙasar ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume.
Ya ce dole ne hukumomin raya yankuna su mayar da hankali kan ayyukan da ke da cikakkun manufofi, ingantaccen tsarin samar da kuɗaɗe da kuma sakamakon da za a iya auna tasirinsa ga al’ummomin da ake yi wa hidima.
Shugaban Ƙasar ya ce “zamanin ayyukan white elephant ya ƙare,” yana mai gargadin cewa babu wani dalili da zai sa hukumomin su zama hanyar ɓarnatar da kuɗaɗen jama’a. Ya kuma yi gargaɗi kan cin hanci da rashawa, tsoma bakin siyasa, wariya da kuma fifita ƙabilanci wajen rabawa da aiwatar da ayyukan raya ƙasa.
Tinubu ya umarci Gwamnatin Tarayya da ta tabbatar da sakin kuɗaɗen da suka wajaba ga hukumomin cikin lokaci, tare da alkawarin ci gaba da ba su goyon bayan siyasa da na kuɗi. Ya kuma buƙaci hukumomin su nemi wasu hanyoyin samun kuɗaɗe, ciki har da zuba hannun jari daga kamfanoni masu zaman kansu, tallafin ƙasashen waje da kuma kuɗaɗen cibiyoyin raya ƙasa.
A game da Arewa ta Tsakiya, Tinubu ya bayyana noma, sarrafa amfanin gona, haƙar ma’adinai, masana’antu, tsaro, ilimi da kiwon lafiya a matsayin muhimman fannoni da ke buƙatar kulawa cikin gaggawa.
Shugaban Ƙasar ya bukaci mahalarta taron da su samar da ingantaccen tsarin raya yankin na dogon lokaci, wanda zai jagoranci ci gaban tattalin arziki, ababen more rayuwa da jin daɗin al’ummar Arewa ta Tsakiya cikin shekaru 20 masu zuwa.
#Tinubu #NCDC #NorthCentral #Development #Nigeria #RenewedHopeAgenda #NexViewTV #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa

Comments
Post a Comment