Trump Ya Yi Watsi Da Shawarar Iran Kan Mashigar Hormuz
Trump Ya Yi Watsi Da Shawarar Iran Kan Mashigar Hormuz
Umar Nusaiba Ibrahim
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya yi watsi da wata shawara da Iran ta gabatar domin sake bude mashigar ruwa ta Hormuz.
Trump ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da yake magana da manema labarai a wajen fadar White House.
Ya ce Iran ta gabatar da shirin da zai ba da damar bude mashigar cikin kwanaki bakwai, amma ya yanke shawarar kin amincewa da shirin.
Trump ya ce Iran na son cimma yarjejeniya domin a bude mashigar cikin gaggawa, yana mai cewa kasar na fuskantar matsin lamba sakamakon halin da ake ciki.
Ya kara da cewa Iran na son a yi yarjejeniya, shi ma yana goyon bayan yin yarjejeniya, amma ya ce bai amince da shawarar da Tehran ta gabatar ba.
Mashigar Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin safarar man fetur a duniya, kuma duk wani cikas ga zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin na iya shafar kasuwancin makamashi da farashin man fetur a duniya.
#Trump #Iran #StraitOfHormuz #US #IranNews #WorldNews #GlobalNews #Oil #CrudeOil #MiddleEast #USA #IranUSA #NexViewTV #BBCHausa #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa

Comments
Post a Comment