2027: ADC Ta Yi Wa Wike Martani, Ta Ce Tsoratarwa Ba Za Ta Lashe Zaɓe Ba
Umar Nusaiba Ibrahim
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Jihar Rivers ta mayar da martani ga kalaman Ministan Abuja, Nyesom Wike, na cewa za ta kayar da mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Rotimi Amaechi, kafin ƙarfe 12 na ranar zaɓe.
Shugaban ADC na jihar, Dr. Chukwudi Dimkpa, ya ce ikon bayyana sakamakon zaɓe yana hannun Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ba Wike ba. Ya ce babu wani ɗan siyasa da zai iya cin zaɓe ta hanyar alfahari, tsoratarwa ko yi wa al’umma alkawuran ƙarya.
Dimkpa ya bayyana kalaman Wike a wani taron karɓar bakuncinsa da aka gudanar a Omagwa, ƙaramar hukumar Ikwerre, a ranar Asabar, a matsayin siyasar da ta wuce gona da iri. Ya kuma yi kira ga al’ummar Rivers da kada su bari wani ya tsoratar da su, su kuma kasance cikin shirin yin zaɓin da ya dace a 2027.
Ya ce zaɓe ba a cin sa da alfahari ko barazana, domin al’umma ce za ta jefa ƙuri’a, sannan a ƙirga ƙuri’un kafin INEC ta bayyana wanda ya yi nasara. Ya kuma soki yadda aka gudanar da taron siyasar a lokacin da Amaechi ke binne mahaifiyarsa, yana mai cewa lokaci ne da ya kamata a nuna tausayi da girmamawa.
ADC ta ce jihar Rivers mallakin kowa ce, kuma babu wani ɗan siyasa da ya mallaki al’umma ko ƙuri’unsu. A nasa ɓangaren, Wike ya shaida wa magoya bayansa cewa dukkan ’yan takarar da Rainbow Coalition ta zaɓa za su yi nasara a zaɓen 2027.
#2027Elections #ADC #Wike #RotimiAmaechi #RiversState #INEC #NigeriaPolitics #RiversPolitics #ADC2027 #NyesomWike #Amaechi #Election2027 #NigerianPolitics #ArewaNews #NexViewTV #RFIHausa #BBCHausa #Arewa24

Comments
Post a Comment