Waɗanne sakonni APC ke son aikawa a tarukan da take yi a jihohi?
Waɗanne sakonni APC ke son aikawa a tarukan da take yi a jihohi?
Daga Zamira Ahmad Nasidi
Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta fara ƙara kaimi wajen shirye-shiryen siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027, inda ta gudanar da wani babban taron siyasa a Kano a ranar Asabar, wanda ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar daga ciki da wajen jihar.
A yayin taron, APC ta karɓi wasu fitattun ‘yan siyasa da magoya bayansu da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar. Jam’iyyar ta ce sama da mutum 136,000 ne suka shiga cikinta, ciki har da Sanata Rufa’i Hanga da tsohon Gwamnan Kano, Sanata Kabiru Gaya.
Taron ya kuma samu halartar gwamnoni, sanatoci da sauran manyan jami’an APC, waɗanda suka bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf. Jiga-jigan jam’iyyar sun kuma jaddada aniyar APC na samun nasara a zaɓen 2027.
Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin taron a matsayin wani yunƙuri na APC na nuna ƙarfin siyasarta, haɗa kan magoya baya da kuma faɗaɗa tasirinta a jihohin da ke da muhimmiyar rawa wajen samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa.
Ɗaya daga cikin manyan saƙonnin taron shi ne ƙara nuna goyon baya ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027. Shugabannin APC sun ce yawan waɗanda ke shiga jam’iyyar da halartar tarukan na nuna cewa goyon bayan Tinubu da manufofin gwamnatinsa na ƙaruwa, yayin da jam’iyyun adawa ke ci gaba da shirye-shiryensu domin tunkarar zaɓen.
#APC #APC2027 #Zaben2027 #Kano #Tinubu #BolaAhmedTinubu #AbbaKabirYusuf #KabiruGaya #RufaiHanga #SiyasarNajeriya #NigeriaPolitics #2027Elections #KanoPolitics #Najeriya #ZabenNajeriya #Siyasa #APCNews #PoliticalNews #NigeriaNews #BreakingNews
#zamira news

Comments
Post a Comment