Yadda Matashi Ya Yanke Yatsarsa Don Kai Wa Boka, Bisa Alkawarin Naira Miliyan 80 a Kano
Yadda Matashi Ya Yanke Yatsarsa Don Kai Wa Boka, Bisa Alkawarin Naira Miliyan 80 a Kano
Daga Zamira Ahmad Nasidi
Wani lamari mai ban mamaki da ya jawo ce-ce-ku-ce a jihar Kano ya kai ga cafke mutane huɗu, bayan zargin wani matashi da yanke ɗaya daga cikin yatsunsa domin kai wa wani boka, bisa alkawarin samun kuɗi har naira miliyan 80.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya gano cewa matashin ya aikata hakan ne bayan wani mutum ya yi masa alkawarin biyan sa makudan kuɗaɗe idan ya samar da yatsar mutum mai rai.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida wa BBC cewa matashin mai suna Yusuf Mahmuda, mai shekaru 27, shi ne ya kai ƙorafi ga ’yan sanda bayan ya ce bai samu kuɗin da aka yi masa alkawari ba.
A cewar CSP Kiyawa, mutumin da ya nemi yatsar ya gaya wa matashin cewa zai biya masa naira miliyan 80 idan ya samo masa yatsar mutum mai rai.
Yadda lamarin ya faru
Kiyawa ya ce bayan matashin ya yi ta ƙoƙarin nemo yatsar wani mutum, amma bai samu ba, sai ya yanke shawarar yanke ɗaya daga cikin yatsunsa domin cika abin da aka buƙata.
«“Mutumin ya ce bayan ya zagaya, ya faki mutane da dama bai samu ba, sai ya yanke shawarar yanke yatsarsa, tun da dai yatsar mutum mai rai ake buƙata,” in ji CSP Kiyawa.»
Sai dai bayan da matashin ya kai yatsar ga mutumin da ya yi masa wannan buƙata, ya ce mutumin ya fara yi masa “wala-wala”, inda daga bisani ya ƙi ba shi kuɗin da aka yi masa alkawari.
Wannan ne ya sa matashin ya garzaya ofishin ’yan sanda domin shigar da ƙorafi.
Rundunar ’yan sandan ta ce binciken da ta gudanar ya kai ga gano wasu mutane da ake zargin suna da hannu a lamarin, ciki har da mutumin da ake zargin ya nemi yatsar da kuma wani da ake zargin boka ne.
A yayin binciken, waɗanda ake zargi sun ba da bayanai kan lamarin, inda kowannensu ya bayyana nasa ɓangaren dangane da zargin da ake yi.
’Yan sanda sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken bayani kan abin da ya faru da kuma irin rawar da kowanne daga cikin waɗanda aka kama ya taka.
Lamarin ya sake haifar da muhawara kan illolin yaudarar mutane da kuma imanin cewa ana iya samun dukiya cikin sauƙi ta hanyar abubuwan camfi ko tsafi.
#Kano #KanoState #Nigeria #YanSanda #Police #LabarinKano #LabaranYau #NairaMiliyan80 #Boka #CrimeNews #BreakingNews #NigeriaNews #HausaNews

Comments
Post a Comment