Yamal: Ba Don Kuɗi Nake Buga Ƙwallo Ba
Yamal: Ba Don Kuɗi Nake Buga Ƙwallo Ba
Samira Ahmad Danketa
Ɗan wasan gefe na Barcelona da tawagar ƙasar Spain, Lamine Yamal, ya bayyana cewa sha’awarsa ga ƙwallon ƙafa ce babban dalilin da ya sa yake buga wasa, ba don samun kuɗi, ƙwallaye ko taimakon zura ƙwallaye ba.
Yamal ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar The Guardian, inda ya ce yana jin daɗin ƙwallon ƙafa sosai idan yana samun damar nuna ƙwarewarsa, taimaka wa ƙungiyarsa da kuma samar wa abokan wasansa damar cin ƙwallo.
Matashin ɗan wasan ya ce baya son ƙididdigar ƙwallayen da ya ci ko taimakon da ya bayar ta zama abin da aka fi mayar da hankali a kansa a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa. Ya ce yawan damuwa da irin waɗannan ƙididdiga na iya rage wa ɗan wasa jin daɗin wasan.
Yamal ya ce: “Ba don kuɗi nake buga ƙwallo ba, ina buga ta ne saboda ina sonta. Ina buga wasa ne don nishaɗi, yin dribbling, yin passes, da kuma taimaka wa ɗan wasan da bai ci ƙwallo ba ya ci, domin farin ciki.”
Yamal ya kuma yi magana kan ganawarsa da fitaccen ɗan wasan Argentina kuma tsohon ɗan wasan Barcelona, Lionel Messi, inda ya ce ya je wurinsa ne domin gode masa bisa irin gudunmawar da ya bayar ga ƙwallon ƙafa. Yamal ya ce a wurinsa, Messi ne mafi kyawun ɗan wasan ƙwallon ƙafa, kuma ganawar tasu ta faru ne kwatsam ba tare da wani shiri na neman shahara ba.
#LamineYamal #Yamal #Barcelona #FCBarcelona #Spain #Football #KwallonKafa #LionelMessi #Messi #LaLiga #FootballNews #LabaranWasanni #NexviewTV #NigerianFootball #HausaNews

Comments
Post a Comment