Yara 26 Sun Mutu a Gobarar Makaranta a Congo
Yara 26 Sun Mutu a Gobarar Makaranta a Congo
Akalla yara 26 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 25 suka jikkata, sakamakon gobara da turmutsitsi da ya tashi a makarantar Ujamaa Primary School da ke birnin Bukavu, gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo.
Gobarar ta tashi ne da safiyar Alhamis yayin da ɗalibai ke cikin karatu. Wasu yara sun tsere ta ƙofofi, yayin da wasu suka tsalle daga bene domin kubuta daga wutar.
Rahoton hukumomi ya ce wasu daga cikin yaran sun mutu sakamakon turmutsitsi da kuma shakewa saboda hayaki. Daga cikin waɗanda suka mutu, 20 ’yan mata ne, yayin da shida maza ne.
Hukumomi da ƙungiyar M23 sun buƙaci a gudanar da bincike domin gano musabbabin gobarar, wadda kuma ta lalata daruruwan gidaje.
Lamarin ya jefa Bukavu cikin babban alhini, yayin da aka ayyana kwanaki uku na zaman makoki domin tunawa da waɗanda suka rasa rayukansu.
#Congo #DRC #Bukavu #GobararMakaranta #Yara #LabaranDuniya #AfricaNews #WorldNews #BreakingNews #SchoolFire #CongoNews #UjamaaPrimarySchool #Tragedy #Education #ZAMIRA news

Comments
Post a Comment