2027: INEC Ta Cire Sunan Pantami Daga Jerin ’Yan Takarar Gwamnan Gombe


 

2027: INEC Ta Cire Sunan Pantami Daga Jerin ’Yan Takarar Gwamnan Gombe


Umar Nusaiba Ibrahim 


Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta cire sunan Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙin Zamani, daga jerin ƙarshe na ’yan takarar gwamnan Jihar Gombe a zaɓen 2027.


Wannan na zuwa ne bayan wata kotu ta soke zaɓen fid-da-gwanin farko na jam’iyyar PDP da ya samar da Pantami a matsayin ɗan takarar gwamna. Duk da cewa sunansa ya bayyana a jerin wucin-gadi da INEC ta fitar ranar 29 ga watan Agusta, bai bayyana a jerin ƙarshe na ’yan takara 16 da hukumar ta wallafa ba.


Pantami, wanda ya sauya sheƙa daga APC zuwa PDP a ranar 19 ga watan Mayu, ya lashe sabon zaɓen fid-da-gwanin jam’iyyar da aka gudanar ranar 29 ga watan Satumba, inda ya samu ƙuri’u 2,054, ya doke Khamisu Ahmed Mailantarki da Usman Aliyu Garry.


Sai dai a ranar 24 ga watan Satumba, Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta soke zaɓen fid-da-gwanin PDP da aka gudanar ranar 26 ga watan Mayu. Haka kuma, hukuncin Kotun Ƙoli kan wasu sassan Dokar Zaɓe ta 2026 ya shafi cancantar jam’iyyu wajen tsayar da ’yan takara.


Kwamishinan INEC na Ƙasa, Mohammed Haruna, ya bayyana a shirin siyasa na Trust TV cewa hukuncin Kotun Ƙoli ya hana jam’iyyu tsayar da ’yan takarar da sunayensu ba sa cikin rajistar mambobin jam’iyyar da aka miƙa wa INEC cikin wa’adin da doka ta tanada.


Daga cikin sunayen da suka bayyana a jerin ƙarshe na INEC akwai Bala Bello Tinka na ADC, Jamilu Isyaku Gwamna na APC da Babayo Ardo Kumo na NDC. Sauran sun haɗa da Zubairu Mu’azu Halilu na LP, Lamela L. Silas na APM, Ibrahim Jalo Abubakar na PRP da Adamu Mohammed Ma’aji na SDP.



#INEC #IsaAliPantami #Pantami #Gombe #Zaben2027 #PDP #APC #SiyasarGombe #SiyasarNajeriya #DokarZabe2026 #NigeriaPolitics #BBCHausa #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa #NexViewTV

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

KANO BRIDE SENTENCED TO DEATH BY HANGING 9 DAYS AFTER WEDDING