2027: Tinubu Zai Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓensa A Kaduna — Yari
2027: Tinubu Zai Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓensa A Kaduna — Yari
Umar Nusaiba Ibrahim
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa na sake tsayawa takara a zaɓen 2027 a jihar Kaduna, a ranar 24 ga Oktoba, kamar yadda Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya bayyana.
Yari ya bayyana hakan ne ranar Juma’a bayan ganawarsa da Shugaba Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Ya ce bayan ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen a Kaduna, tawagar za ta wuce Fatakwal da ke jihar Ribas, da kuma Maiduguri a jihar Borno domin ci gaba da kamfen ɗin.
A cewarsa, shugaban ƙasar ya amince da jadawalin yaƙin neman zaɓen, wanda za a bayyana wa jama’a bayan ƙaddamar da kwamitin a ranar 14 ga Oktoba.
Yari ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa kan damar da Tinubu ke da ita ta samun nasara a zaɓen, inda ya yi iƙirarin cewa shugaban ƙasar yana da goyon baya a jihohi da dama na Arewa da Kudancin Najeriya.
Ya yi ikirarin cewa manyan abokan hamayyar Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi, ba su samu gagarumin goyon bayan jama’a a faɗin ƙasar ba.
Yari ya jaddada cewa samun nasarar zaɓen shugaban ƙasa na buƙatar goyon bayan jama’a daga sassan Arewa da Kudu, yana mai cewa goyon bayan yanki guda ɗaya ba zai wadatar ba.
Ya kuma kare manufofin gwamnatin Tinubu, inda ya ce an samu ci gaba wajen tunkarar ƙalubalen tattalin arzikin Najeriya.
#Tinubu #AbdulazizYari #APC #Zaben2027 #NigeriaPolitics #AtikuAbubakar #PeterObi #Kaduna #Maiduguri #PortHarcourt #YaƙinNemanZaɓe #SiyasarNajeriya #BBCHausa #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa #NexViewTV

Comments
Post a Comment