ABU Zariya Ta Zama Ta Uku Mafi Matsayi A Tsakanin Jami’o’in Gwamnati A Najeriya
ABU Zariya Ta Zama Ta Uku Mafi Matsayi A Tsakanin Jami’o’in Gwamnati A Najeriya
Umar Nusaiba Ibrahim
Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ABU, ta ƙara samun matsayi a fagen ilimi na duniya, bayan da ta zama jami’ar gwamnati ta uku mafi matsayi a Najeriya a sabon jadawalin Times Higher Education (THE) World University Rankings 2027.
A jadawalin, ABU ta zo ta huɗu a cikin jami’o’in Najeriya baki ɗaya, inda aka sanya ta cikin rukunin jami’o’in da ke matsayi na 1,001 zuwa 1,200 a duniya. A wannan rukuni akwai kuma Jami’ar Bayero, Landmark University da Jami’ar Ilorin.
Bugu da ƙari, ABU ta zo ta huɗu a Najeriya sannan ta 42 a Afirka a jadawalin UI GreenMetric World University Ranking 2026, inda ta samu maki 5,552.5. A duniya kuwa, ta kasance ta 1,032 cikin jami’o’i 2,016 daga ƙasashe 110 da suka shiga gasar.
Jadawalin THE yana auna jami’o’i ne ta fannoni 17 da suka haɗa da ingancin koyarwa, muhalli da ingancin bincike, haɗin gwiwa da masana’antu da kuma alaƙar jami’a da ƙasashen duniya. A Najeriya, ABU ta zo ta uku a fannin koyarwa da kuma ta uku a fannin hulɗa da masana’antu, wanda ya haɗa da samun kuɗaɗen masana’antu da mallakar haƙƙin ƙirƙira.
A ɓangaren GreenMetric kuwa, ana duba yadda jami’o’i ke tafiyar da harkokin kare muhalli da samar da muhallin karatu mai ɗorewa. ABU ta samu maki 1,300 a makamashi da sauyin yanayi, 905 a ruwa, 800 a sufuri, 700 a ilimi, 685 a gine-gine da ababen more rayuwa, 612.5 a shugabanci da fasahar zamani, sannan 550 a kula da shara.
Wadannan sakamako sun ƙara nuna yadda ABU ke samun matsayi a fannonin ilimi, bincike, hulɗa da masana’antu da kuma kare muhalli. Tun farkon shekarar 2026, jami’ar ta samu wasu matsayi a jadawalin jami’o’in duniya, ciki har da matsayi na uku a Najeriya a QS World University Rankings 2027, tare da matsayi na huɗu a jadawalin Centre for World University Rankings da kuma na uku a jadawalin U.S. News Best Global Universities.
#NexViewTV #ABUZaria #AhmaduBelloUniversity #Zaria #Nigeria #Education #JamiA #Arewa #ArewaNews #LabaranArewa #HausaNews #BBCHausa #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa #FreedomRadioKano #DailyTrust #Ilimi #LabaranKasa

Comments
Post a Comment