Amurka Na Shirin Ƙara Tuhume-tuhumen Azabtarwa Kan Maduro Da Matarsa

 



Amurka Na Shirin Ƙara Tuhume-tuhumen Azabtarwa Kan Maduro Da Matarsa


Umar Nusaiba Ibrahim 


Masu gabatar da ƙara a Amurka na shirin ƙara wasu tuhume-tuhume kan tsohon shugaban Venezuela, Nicolás Maduro, da matarsa Cilia Flores, bisa zargin azabtar da wasu ’yan Amurka da aka tsare a hannun gwamnatin Venezuela, kamar yadda CNN ta ruwaito.


Maduro da Flores sun riga sun fuskanci tuhume-tuhume a Amurka da suka shafi safarar miyagun ƙwayoyi da kuma mallakar makamai, bayan da sojojin Amurka suka kama su a wani samame da suka kai gidansu a Caracas a watan Janairu.


Rahoton CNN, wanda ya ambaci wasu majiyoyi da ke da masaniya kan binciken, ya ce sabbin tuhume-tuhumen azabtarwar sun shafi zargin tsare sama da ’yan Amurka 12 ba bisa ka’ida ba a Venezuela a lokacin mulkin Maduro.


Rahoton ya kuma ce masu gabatar da ƙara na duba yiwuwar tuhumar wasu mutane da ake zargi da hannu wajen azabtar da ’yan Amurkan.


CNN ta ce ana iya sanar da sabbin tuhume-tuhumen tun ranar Alhamis, sai dai masu gabatar da ƙara a Amurka ba su yi tsokaci kan rahoton ba lokacin da AFP ta tuntube su.


A halin yanzu, Maduro da Flores suna tsare a wani gidan yari da ke Brooklyn, kuma ana sa ran za su fuskanci shari’a a birnin New York a watan Yunin shekara mai zuwa.


Masu gabatar da ƙara a Amurka na zargin Maduro da amfani da ikon gwamnati wajen karewa da kuma taimakawa safarar miyagun ƙwayoyi, tare da haɗin gwiwa da ƙungiyoyin masu safarar ƙwayoyi wajen shigar da tarin hodar iblis zuwa Amurka.


Maduro ya musanta dukkan tuhume-tuhume huɗu da ake masa, yayin da Flores ita ma ta musanta tuhume-tuhume uku da ake mata.


Haka kuma, ana sa ran Flores za ta gurfana a gaban kotu domin sauraron bukatarta ta sauya daga tsare ta zuwa zaman gidan yari na gida saboda matsalolin zuciya da ake zargin tana fama da su.



#Maduro #Venezuela #USA #America #CiliaFlores #NicolasMaduro #USJustice #VenezuelaCrisis #WorldNews #InternationalNews #BBCHausa #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa #NexViewTV

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

KANO BRIDE SENTENCED TO DEATH BY HANGING 9 DAYS AFTER WEDDING