Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Aikin Hanyar Kilomita 95 A Tsafe
Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Aikin Hanyar Kilomita 95 A Tsafe
Umar Nusaiba Ibrahim
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da aikin gina hanyar da ta kai tsawon kilomita 95 a ƙaramar hukumar Tsafe, yana mai cewa aikin zai taimaka wajen inganta ayyukan tsaro, sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a da kayayyaki, tare da bunƙasa harkokin tattalin arziki a yankin.
Aikin ya haɗa da hanyoyin da za su haɗa ’Yandoton Daji, Cediya, Doka, ’Yan Waren Daji, Hayin Alhaji Bedi, Unguwar Joji da ’Yankuzo da garin Tsafe, tare da gina gadoji guda biyar. Za a gudanar da aikin ne cikin matakai biyu, inda matakin farko zai kasance kilomita 47, yayin da na biyu zai kai kilomita 48.
Kamfanin SKY Construction Company ne zai gudanar da matakin farko, yayin da Setraco Construction Company Limited za ta ɗauki nauyin mataki na biyu. Gwamna Lawal ya ce aikin na da muhimmanci musamman saboda zai haɗa al’ummomin da yawancinsu ke dogaro da noma, wanda ke taka muhimmiyar rawa wajen tattalin arzikin jihar.
Ya ce sabuwar hanyar za ta ƙara inganta zirga-zirgar jami’an tsaro da kuma ba su damar gaggauta kai ɗauki yayin fuskantar barazana ko hare-hare. A cewarsa, aikin wani ɓangare ne na shirin gwamnatinsa na farfaɗo da ababen more rayuwa da kuma sake haɗa al’ummomin da suka daɗe suna fama da ƙarancin hanyoyin sufuri.
Gwamnan ya ce kyawawan hanyoyi na da muhimmiyar rawa wajen samar da zirga-zirga cikin aminci, sauƙaƙa safarar kayayyaki da bunƙasa tattalin arziki. Ya kuma ba da umarni ga Ma’aikatar Ayyuka da Samar da Ababen More Rayuwa ta jihar da ta tabbatar da ingantaccen sa ido, bin ƙa’idojin aikin injiniya da kuma tabbatar da an kammala aikin cikin lokacin da aka tsara.
Lawal ya kuma gargadi kamfanonin da ke gudanar da ayyukan gwamnati da su tabbatar da an samu ƙimar kuɗin da aka kashe tare da samar da ayyuka masu ɗorewa. Ya bayyana fatansa cewa hanyar za ta ƙarfafa tsaro, inganta sufuri da kuma ƙara haɗin kan al’ummomin Tsafe da kewayenta.
#NexViewTV #Zamfara #DaudaLawal #Tsafe #RoadProject #ZamfaraNews #LabaranNajeriya #ArewaNews #Arewa #BBCHausa #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa #DailyTrust

Comments
Post a Comment