Gwamnonin Arewa Maso Gabas Sun Nemi Tinubu Ya Farfaɗo da Aikin Haƙo Mai a Borno


 


Gwamnonin Arewa Maso Gabas Sun Nemi Tinubu Ya Farfaɗo da Aikin Haƙo Mai a Borno


Umar Nusaiba Ibrahim 


Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Maso Gabas ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta farfaɗo da aikin bincike da haƙo ɗanyen mai a Jihar Borno.


Gwamnonin sun bayyana wannan buƙata ne yayin taronsu na 13 da aka gudanar a Maiduguri, inda suka tattauna kan batutuwan tsaro, ci gaba da bunƙasa tattalin arzikin yankin.


Sun buƙaci gwamnati ta dawo da aikin binciken man fetur a Ƙananan Hukumomin Magumeri da Gubio, inda aka fara aikin a baya kafin daga bisani a dakatar da shi.


Haka kuma, gwamnonin sun yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan farfaɗo da aikin haƙo mai na Kolmani da ke Jihar Gombe, da kuma sauran manyan ayyukan raya ƙasa, ciki har da layin dogo daga Maiduguri da kuma babbar hanyar Akwanga zuwa Maiduguri.


Gwamnonin sun kuma yi kira da a gaggauta kammala aikin tashar samar da wutar lantarki ta Mambila, tare da ƙara yawan tashoshin CNG da LNG a yankin Arewa Maso Gabas.


Sun ce za su ƙara ƙaimi wajen haɗa kai wajen yaƙi da rashin tsaro, inganta harkar ilimi da koyar da matasa sana’o’i, tare da tallafa wa hukumomin da ke yaƙi da sare itatuwa.


An tsara gudanar da taron gwamnonin na gaba a Jihar Gombe, a ranakun 18 da 19 ga Disamba 2026.



#ArewaMasoGabas #Borno #Maiduguri #ManFetur #HaƙoMai #Tinubu #GwamnoninArewa #TattalinArziƙi #CiGaba #Tsaro #CNG #LNG #Mambila #Kolmani #Nigeria #NexViewTV #BBCHausa #RFIHausa #Arewa24 #ArewaRadio #FreedomRadioKano #DailyTrust #PUNCH #DDLHausa

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

KANO BRIDE SENTENCED TO DEATH BY HANGING 9 DAYS AFTER WEDDING