Hamma Saleh, Abokin Hamayyar Pantami, Ya Fice Daga PDP Ya Koma APC
Hamma Saleh, Abokin Hamayyar Pantami, Ya Fice Daga PDP Ya Koma APC
Umar Nusaiba Ibrahim
Tsohon mai neman takarar gwamnan jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Alhaji Abdulkadir Hamma Saleh, ya yi murabus daga jam’iyyar tare da komawa jam’iyyar APC mai mulki, gabanin zaɓen gwamna na shekarar 2027.
Hamma Saleh, wanda ya fafata da tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, a zaɓen fitar da gwani na PDP, ya sanar da matakin nasa ne cikin wata sanarwa da aka rabawa ’yan jarida a Gombe.
Bayan sanar da ficewarsa daga PDP, Hamma Saleh ya yi kira ga magoya bayansa a faɗin jihar da su bi shi zuwa APC, tare da mara wa ’yan takarar jam’iyyar baya a dukkan matakan gwamnati.
Ficewarsa na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauyen kawance a siyasar jihar Gombe, yayin da jam’iyyu da masu neman takara ke ƙoƙarin ƙarfafa matsayinsu gabanin babban zaɓen 2027.
Matakin na Hamma Saleh na da muhimmanci musamman duba da takaddamar da aka daɗe ana yi kan tikitin takarar gwamnan PDP, inda aka ƙalubalanci sakamakon zaɓen fitar da gwani na farko da ya shafi Pantami a kotu, daga bisani aka sake gudanar da zaɓen.
Ficewar Hamma Saleh na iya ƙara sauya yanayin siyasar jihar, yayin da PDP ke fuskantar ƙalubalen cikin gida gabanin zaɓe mai zuwa. Tsohon mai neman takarar ya kuma sake kira ga magoya bayansa da su haɗa kai da APC domin mara wa jam’iyyar baya a fafatawar siyasar da ke tafe.
#HammaSaleh #IsaAliPantami #PDP #APC #SiyasarGombe #Zaben2027 #SiyasarNajeriya #GombeState #Labarai #BBCHausa #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa #NexViewTVI

Comments
Post a Comment