IMF Ta Gargadi Gwamnatin Tarayya Kan Maido Da Tallafin Man Fetur
IMF Ta Gargadi Gwamnatin Tarayya Kan Maido Da Tallafin Man Fetur
Umar Nusaiba Ibrahim
Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya shawarci Gwamnatin Tarayya da kada ta dawo da tallafin man fetur ga kowa, maimakon haka ya kamata ta samar da tallafi na musamman ga iyalai masu ƙaramin ƙarfi domin rage musu raɗaɗin tsadar makamashi.
IMF ta bayyana cewa tallafin man fetur ga kowa yana kashe kuɗaɗen gwamnati masu yawa, kuma galibi masu kuɗi ne ke cin gajiyarsa fiye da masu ƙaramin ƙarfi. Ta kuma yi gargaɗin cewa dawo da tallafin na iya ƙara matsin lamba kan kuɗaɗen gwamnati, musamman a lokacin da kuɗin biyan basussuka ke ƙaruwa.
Daraktan sashen kula da harkokin kuɗaɗen gwamnati na IMF, Rodrigo Valdés, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai kan rahoton asusun a taron shekara-shekara na IMF da Bankin Duniya na shekarar 2026, da aka gudanar a Bangkok, ƙasar Thailand.
Valdés ya ce kare al’umma daga tsadar rayuwa ba yana nufin gwamnati dole ta riƙa hana farashin man fetur tashi ba. Ya bayyana cewa tallafin makamashi da matakan hana farashi bin yanayin kasuwa sun jawo wa ƙasashe kashe kuɗaɗen da suka kai tsakanin kashi ɗaya zuwa ɗaya da rabi cikin ɗari na GDP a shekarar 2026.
Ya shawarci gwamnatoci da su fi mayar da hankali kan shirye-shiryen tallafa wa jama’a masu buƙata, ta hanyar amfani da bayanan iyalai domin gano waɗanda suka fi buƙatar taimako. A nata ɓangaren, Gwamnatin Tarayya ta sanar da rangwamen kuɗin man fetur na tsawon kwanaki 30 a gidajen mai na kamfanin NNPC, inda aka ba masu safarar jama’a fifiko domin rage tasirin tashin farashin man fetur.
#IMF #FuelSubsidy #ManFetur #NigeriaEconomy #EconomicReforms #TsadarRayuwa #GwamnatinTarayya #NNPC #Inflation #Poverty #RodrigoValdes #WorldBank #NigeriaNews #BBCHausa #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa #NexViewTV

Comments
Post a Comment