INEC Na Nazarin Hukuncin Kotun Ƙoli Kan Dokar Zaɓe
INEC Na Nazarin Hukuncin Kotun Ƙoli Kan Dokar Zaɓe
Umar Nusaiba Ibrahim
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta ce ta fara nazarin hukuncin Kotun Ƙoli kan wasu tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta shekarar 2026, waɗanda ka iya shafar cancantar wasu ‘yan takara gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Kotun Ƙolin ta tabbatar da ingancin sashe na 77 da 84 na Dokar Zaɓe ta 2026, a hukuncin da ta yanke ranar Alhamis, bayan sauraron ƙorafe-ƙorafen Jam’iyyar Zenith Labour Party, ZLP, da Social Democratic Party, SDP, kan cancantar tsayawa takara a zaɓen fidda gwani.
Hukuncin ya haifar da cece-kuce kan yadda zai shafi ‘yan siyasar da suka sauya sheka zuwa wasu jam’iyyu bayan sun gaza samun tikitin takara a jam’iyyun da suke ciki tun farko.
A Gombe, ana ta nuna damuwa kan makomar Farfesa Isa Ali Pantami, sakamakon lokacin da ya sauya sheka daga Jam’iyyar APC zuwa PDP. Haka kuma, hukuncin ya jawo tambayoyi kan cancantar tsohon Sufeto-Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Abubakar Adamu, a Jihar Nasarawa, wanda ya maye gurbin ɗan takarar SDP na gwamna, Adamu Angba, bayan janyewarsa daga takarar.
Sai dai da yake magana a wani taron manema labarai a Abuja, Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce hukumar ta samu korafe-korafe daga wasu jam’iyyun siyasa, ‘yan takara da kuma wasu mambobin Majalisar Dokoki ta Ƙasa, kan abin da hukuncin Kotun Ƙolin zai iya haifarwa.
Farfesa Amupitan ya ce INEC ta karɓi kwafin hukuncin Kotun Ƙoli da aka tabbatar da ingancinsa a ranar Talata, kuma yanzu haka tana nazarinsa kafin yanke shawarar matakin da ya dace ta ɗauka.
Daga cikin ‘yan takarar da batun ya shafa akwai ɗan takarar gwamnan Jihar Rivers na APC, Kingsley Chinda; ɗan takarar Sanatan Delta ta Tsakiya na Nigeria Democratic Congress, NDC, Ovie Omo-Agege; tsohon Gwamnan Jihar Cross River kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na PRP, Donald Duke; da tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Delta, Victor Ochei.
INEC ta ce sakamakon nazarin hukuncin zai taimaka wajen fayyace tasirinsa ga ‘yan takarar da abin ya shafa, jam’iyyun siyasa da kuma shirye-shiryen hukumar na babban zaɓen 2027.
#INEC #ElectoralAct2026 #SupremeCourt #2027Elections #NigeriaPolitics #Election2027 #INECUpdates #APC #PDP #SDP #ZLP #PRP #NigerianPolitics #PoliticalNews #NigeriaNews #DailyTrust #PUNCH #BBCHausa #FreedomRadioKano #Legit #DDLHausa #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa

Comments
Post a Comment