INEC Ta Gargadi Jama’a Kan Jerin Ƙarya Na ’Yan Takarar Gwamnoni
INEC Ta Gargadi Jama’a Kan Jerin Ƙarya Na ’Yan Takarar Gwamnoni
Umar Nusaiba Ibrahim
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta gargaɗi ’yan Najeriya kan wani saƙo na bogi da ke yawo a intanet, wanda ke ɗauke da jerin sunayen ’yan takarar gwamna a jihohi shida.
Jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Zamfara, Gombe, Delta, Plateau, Yobe da Kano. Hukumar ta bayyana sanarwar a matsayin ta ƙarya, tare da jaddada cewa ba ita ce ta fitar da ita ba.
INEC ta buƙaci jama’a da su yi watsi da sanarwar, tare da guje wa sake yaɗa ta, domin kada ta ruɗi mutane. Ta kuma bayyana cewa ba ta fitar da wata sanarwa ta musamman kan ’yan takarar gwamna a waɗannan jihohi ba.
Hukumar ta shawarci ’yan Najeriya da su riƙa tantance sahihancin bayanan zaɓe ta hanyoyin sadarwarta na hukuma, ciki har da shafinta na intanet da kuma sahihan shafukanta na sada zumunta.
INEC ta sake jaddada cewa za ta ci gaba da samar da sahihan bayanai kan harkokin zaɓe, tare da kira ga jama’a da su dogara da majiyoyi masu inganci domin guje wa yaɗa bayanan ƙarya.
#INEC #FakeNews #ElectionNews #Zaben2027 #SiyasarNajeriya #Zamfara #Gombe #DeltaState #PlateauState #Yobe #Kano #ElectionInformation #FactCheck #BBCHausa #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa #NexViewTV

Comments
Post a Comment