Masu Zuba Jari Daga Ƙasashe Sama Da 90 Sun Nuna Sha’awar Sayen Hannun Jari A Matatar Dangote
Masu Zuba Jari Daga Ƙasashe Sama Da 90 Sun Nuna Sha’awar Sayen Hannun Jari A Matatar Dangote
Umar Nusaiba Ibrahim
Matatar Man Fetur da Kayayyakin Sinadarai ta Dangote ta sanar da cewa shirin sayar da hannun jarinta ga jama’a a karon farko ya jawo hankalin masu zuba jari daga ƙasashe sama da 90 na duniya, ciki har da ƙasashen Afirka 51 daga cikin 54.
A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana cewa yawan masu sha’awar sayen hannun jarin ya nuna yadda masu zuba jari ke ƙara amincewa da masana’antun da ’yan Afirka ke ginawa da kuma burin al’ummar nahiyar na mallakar manyan masana’antun da ke cikinta.
Kamfanin ya ce wannan sayar da hannun jari ya kafa sababbin tarihi a kasuwannin hada-hadar kuɗi, inda ya karya tarihin kasuwar Najeriya tun a ranar farko da aka buɗe sayarwar. Haka kuma, cikin kwanaki 10 na farko, ya zarce tarihin da aka taɓa samu a nahiyar Afirka. Masu sha’awar sun haɗa da ’yan kasuwa, asusun fansho, manyan cibiyoyin zuba jari da masu kula da kadarorin kuɗi.
Babban jami’in kuɗi na rukunin kamfanonin Dangote, Murat Erden, ya ce wannan dama ta wuce tara kuɗaɗen jari kawai, domin tana bai wa ’yan Afirka da sauran masu zuba jari damar mallakar wani muhimmin kamfani da ke da tasiri wajen bunƙasa masana’antu a nahiyar. Ya ƙara da cewa mutane da cibiyoyi daga ƙasashen Afirka sun nuna imanin cewa ya kamata ’yan nahiyar su amfana da ci gaban masana’antu tare da mallakar hannun jari a cikinsu.
Rahoton kuɗin kamfanin ya nuna cewa a cikin watanni tara da suka ƙare ranar 30 ga Satumba, 2026, matatar ta samu kuɗin shiga na dala biliyan 22.5, tare da ribar dala biliyan 4.7. Wannan ya nuna sauyi mai yawa idan aka kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2025, lokacin da kamfanin ya yi asarar dala miliyan 117.2. Kuɗin shigarsa ya ƙaru da kashi 144 cikin 100, daga dala biliyan 9.2 zuwa dala biliyan 22.5.
Kamfanin ya kuma bayyana cewa ya inganta yanayin kuɗaɗensa, inda ya sauya daga bashin da ya haura kadarorinsa da dala biliyan 1.73 a watan Satumba na 2025 zuwa samun rarar kuɗi ta dala miliyan 651 a watan Satumba na 2026. Murat Erden ya ce sakamakon da kamfanin ke samu yanzu ya zarce hasashen da aka yi amfani da shi wajen tantance ƙimar hannun jarin da ake sayarwa.
Ana sa ran rufe sayar da hannun jarin a ranar 27 ga Oktoba, 2026. Kamfanin ya ce ya ƙara ƙaimi wajen wayar da kan masu zuba jari a muhimman kasuwanni, domin bai wa mutane da dama damar shiga shirin. Ya kuma jaddada cewa a halin yanzu babu shirin ƙara wa’adin sayarwar.
#DangoteRefinery #AlikoDangote #DangoteGroup #HannunJari #ZubaJari #TattalinArziki #Kasuwanci #Nigeria #Africa #IPO #FinancialMarkets #BBCHausa #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa #NexViewTV

Comments
Post a Comment