Ojudu Ya Bayyana Yadda Hatsari Ya Kusa Hallaka Shi Da Tinubu A Third Mainland Bridge
Ojudu Ya Bayyana Yadda Hatsari Ya Kusa Hallaka Shi Da Tinubu A Third Mainland Bridge
Umar Nusaiba Ibrahim
Tsohon mai taimaka wa shugaban ƙasa kuma ɗan jarida, Sanata Babafemi Ojudu, ya bayyana yadda shi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu suka tsallake rijiya da baya a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a gadar Third Mainland Bridge da ke Legas, jim kaɗan kafin Tinubu ya zama gwamnan jihar.
Ojudu ya bayyana hakan ne a cikin wata wasiƙa a buɗe da ya rubuta wa Shugaba Tinubu yayin bikin cikar Najeriya shekaru na samun ’yancin kai. A cikin wasiƙar, ya kuma buƙaci shugaban ƙasar da ya sake duba wasu manufofin gwamnati da ya ce sun ƙara tsananta rayuwa ga miliyoyin ’yan Najeriya.
A cewarsa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:30 na dare, yayin da shi da Tinubu ke dawowa daga gidan wani babban jami’in tsaro a Ikoyi. Ya ce direban Tinubu a lokacin, marigayi Mustapha, ya yi barci yayin tuki, lamarin da ya sa motar ta buge katangar gadar. Sai dai su biyun sun tsira da rayukansu.
Ojudu ya ce bayan faruwar hatsarin, Tinubu ya umarce shi da ya tuka motar zuwa Alausa, duk da cewa bai taɓa tuka motar da ke amfani da automatic transmission ba a baya. Ya ce duk da haka, ya yi nasarar kai su inda suke son zuwa.
Ya bayyana cewa ya tuna da wannan lamari ne domin nuna tsawon tarihin alaƙarsa da Tinubu, wadda ta samo asali tun lokacin gwagwarmayar adawa da mulkin soja da kuma yakin neman zaɓen Tinubu na zama gwamnan Legas. Ojudu ya ce kafin zaɓen, ya kai Tinubu wajen wani babban jami’in tsaro, Ibrahim Solomon, saboda fargabar cewa za a iya tafka magudi a zaɓen.
A cewar Ojudu, Solomon ya tabbatar musu cewa hukumomin tsaro za su tabbatar da adalci, kuma daga baya ya cika wannan alƙawari. Bayan Tinubu ya yi nasara, Ojudu ya ce ya taimaka wajen tafiyar da kwamitocin mika mulki da shirye-shiryen rantsar da sabuwar gwamnati, amma ya ƙi karɓar wani muƙami a gwamnatin.
Ya ce ya zaɓi komawa aikin jarida ne saboda ya yi imanin cewa Tinubu na buƙatar aƙalla mutum ɗaya a wajen gwamnati da zai iya faɗa masa gaskiya ba tare da neman wata riba ko wata alfarma ta kansa ba. Ojudu ya ce wannan ce rawar da ya yi ƙoƙarin takawa a tsawon shekaru takwas da Tinubu ya yi a matsayin gwamnan Legas.
Ojudu ya kuma bayyana cewa a lokacin tsohon Shugaban Ma’aikatan Gwamnan Legas, Alhaji Lai Mohammed, kan gan shi a ofishin gwamna, inda yake yi masa raha da cewa, “Opposition ɗinmu ya zo. Me muka sake yi ba daidai ba?”
Ya ce a irin wannan yanayi ne ya yanke shawarar rubuta wasiƙar a buɗe ga Tinubu, duk da cewa dangantakarsu ta samu tangarda da kuma cewa bai goyi bayan takarar Tinubu ta shugaban ƙasa a shekarar 2023 ba. Ojudu ya ce tun daga shekarar 2022 bai sake ganawa da Tinubu ba, kuma ya fito fili ya bayyana cewa bai yi aiki domin ganin Tinubu ya ci zaɓen 2023 ba, sannan bai zaɓe shi ba.
Sai dai ya ce wasu wa’azuzzuka biyu da ya ji kwanan nan kan matsalar yunwa da talauci ne suka sa ya yanke shawarar bayyana damuwarsa ga shugaban ƙasa a bainar jama’a.
#NexViewTV #BabafemiOjudu #BolaTinubu #Nigeria #ThirdMainlandBridge #Lagos #SiyasarNajeriya #LabaranNajeriya #ArewaNews #BBCHausa #DailyTrust

Comments
Post a Comment