Shugaban Hukumar Lafiya Ta Bauchi Da ’Ya’yansa Hudu Sun Mutu A Hatsarin Mota
Shugaban Hukumar Lafiya Ta Bauchi Da ’Ya’yansa Hudu Sun Mutu A Hatsarin Mota
Umar Nusaiba Ibrahim
Shugaban Hukumar Kula da Tsarin Gudummawar Kuɗin Lafiya ta Jihar Bauchi (BASHCMA), Alhaji Ibrahim Ladan Duguri, ya rasu tare da ’ya’yansa huɗu sakamakon wani hatsarin mota da ya faru a Yalwan Duguri, cikin Ƙaramar Hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi.
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ne ya tabbatar da rasuwar, inda ya bayyana alhini da matuƙar baƙin ciki kan wannan mummunan lamari. Gwamnan ya bayyana rasuwar Alhaji Ibrahim Ladan Duguri a matsayin babban rashi ga jihar, musamman ɓangaren lafiya, saboda irin gudummawar da ya bayar wajen inganta hanyoyin samun kulawar lafiya ga al’umma.
A cikin saƙon ta’aziyyar da mai ba gwamnan shawara kan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Mukhtar Gidado, ya sanya wa hannu, gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, majalisar masarautar Duguri, abokansa, abokan aikinsa da daukacin al’ummar jihar Bauchi. Ya kuma yi addu’ar Allah Ya ba Suleiman, ɗaya daga cikin ’ya’yan mamacin da rahotanni suka ce ya tsira daga hatsarin, cikakkiyar lafiya da ƙarfi.
Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tsarin inshorar lafiya na jihar da kuma faɗaɗa damar samun kulawar lafiya, musamman ga masu ƙaramin ƙarfi. Ya kuma yaba da gudummawar da marigayin ya bayar a ƙungiyoyin likitocin jihar da ke kula da mahajjata a lokacin aikin Hajji a ƙasar Saudiyya.
Gwamnan ya ƙara da cewa, baya ga kasancewarsa ma’aikacin gwamnati mai kishin al’umma, Alhaji Ibrahim Ladan Duguri babban abokinsa ne kuma abokin karatunsa. Ya ce rasuwarsa ba kawai babban rashi ba ne ga jihar, har ma da shi kansa, saboda dangantakar abota da zumuncin da ke tsakaninsu. Ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa mamacin da ’ya’yansa, Ya karɓi kyawawan ayyukansu, Ya kuma sanya su a Aljannatul Firdaus.
An tsara gudanar da sallar jana’izar mamacin a fadar Dagacin Yalwan Duguri da ƙarfe 11:00 na safe ranar Lahadi. Gwamnan ya kuma yi kira ga al’ummar Bauchi da su sanya iyalan mamatan a cikin addu’o’insu, tare da ba su goyon baya da ta’aziyya a wannan lokaci na baƙin ciki.
#Bauchi #IbrahimLadanDuguri #BalaMohammed #HatsarinMota #BASHCMA #Alkaleri #Labarai #LabarinBauchi #NigeriaNews #BBCHausa #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa #NexViewTV

Comments
Post a Comment