Takaddama Tsakanin Gwamnati Da Masu Sarrafa Shinkafa Kan Farashi
Takaddama Tsakanin Gwamnati Da Masu Sarrafa Shinkafa Kan Farashi
Umar Nusaiba Ibrahim
Gwamnatin Tarayya da masu sarrafa shinkafa a Najeriya sun samu saɓani kan farashin shinkafar da aka sarrafa a cikin gida, inda gwamnati ke ganin farashin ya yi yawa, yayin da masu sarrafa shinkafar ke cewa tsadar kayan masarufi da kuɗaɗen sarrafa ta ne suka jawo hakan.
Gwamnatin ta ce farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50, wanda a halin yanzu yake tsakanin naira 60,000 zuwa 67,000, ya yi tsada, inda take ganin ya kamata a sayar da shi tsakanin naira 55,000 zuwa 57,000.
A wani taro da aka gudanar a ranar Talata, 6 ga Oktoba, 2026, Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Abubakar Kyari, tare da ƙaramin Ministan Noma, Dakta Aliyu Sabi Abdullahi, sun tattauna da shugabannin ƙungiyoyin masu sarrafa shinkafa da manoma domin nemo mafita kan matsalar farashin.
Gwamnatin ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa matsakaicin kuɗin samar da buhun shinkafa ya kai naira 49,389.23. Saboda haka, ta bayyana farashin da ake sayar da shi a kasuwa a matsayin wanda ya yi yawa idan aka kwatanta da kuɗin samar da shi.
Sai dai shugabannin masu sarrafa shinkafa sun ƙalubalanci wannan matsaya, inda suka ce tsadar paddy, wato shinkafar da ba a sarrafa ba, farashin dizal, wutar lantarki, taki da sauran kayan aiki na daga cikin abubuwan da ke ƙara musu kuɗin samarwa.
Shugaban Ƙungiyar Masu Sarrafa Shinkafa ta Najeriya (RIPAN), Mohammed Abubakar Maifata, ya ce ba za a iya rage farashin shinkafa yadda gwamnati ke so ba tare da magance matsalolin da ke damun masu sarrafawa da manoma ba.
Ya kuma nuna damuwa kan shigo da shinkafa daga ƙasashen waje, yana mai cewa hakan na ƙara wa masana’antun cikin gida matsin lamba, tare da rage musu damar yin gogayya a kasuwa.
Maifata ya ce farashin shinkafar da ba a sarrafa ba shi ne babban abin da ke ƙayyade kuɗin da ake kashewa wajen samar da shinkafar da ake sayarwa a kasuwa. Ya ƙara da cewa manoma na kashe kuɗaɗe masu yawa wajen sayen taki da man fetur, wanda ke ƙara musu kuɗin noma.
A nasa ɓangaren, Manajan Daraktan Kamfanin Umza Rice Mills da ke Kano, Alhaji Abubakar Muhammad, ya ce masana’antun sarrafa shinkafa ba za su iya rage farashin da kansu ba matuƙar kuɗin samarwa bai ragu ba.
Ya bayyana cewa kamfanin na kashe kusan naira miliyan 100 a wata wajen biyan kuɗin wutar lantarki, baya ga kuɗin dizal da ake amfani da shi wajen gudanar da janareto saboda rashin ingancin wutar lantarki.
Haka kuma, masu sarrafa shinkafar sun ce matsalar tsaro a wasu yankunan noma, ƙarancin shinkafar da ba a sarrafa ba, tsadar sufuri da rashin wadataccen wutar lantarki na kawo cikas ga samar da shinkafa a ƙasar.
A saboda haka, sun buƙaci gwamnati ta taimaka wa manoma da masana’antun sarrafa shinkafa ta hanyar rage haraji, samar da rance mai sauƙin biya, inganta wutar lantarki da hanyoyin sufuri, tare da magance matsalar tsaro a yankunan noma.
Wasu masana tattalin arziki kuwa sun gargaɗi gwamnati kan ɗora wa kasuwa farashi kai tsaye, suna mai cewa hakan na iya rage sha’awar manoma da masu sarrafa shinkafa na ci gaba da saka jari a harkar.
Masanin tattalin arziki, Ibraheem Maigari, ya ce ya kamata gwamnati ta fi mayar da hankali wajen rage kuɗaɗen noma da sarrafa shinkafa, maimakon tilasta farashin sayarwa.
Ya ce ƙara yawan shinkafar da ake nomawa a cikin gida, inganta hanyoyin ban ruwa, samar da rance mai sauƙi da inganta tsaro na daga cikin matakan da za su taimaka wajen rage farashi cikin ɗorewa.
A halin da ake ciki, masu ruwa da tsaki sun amince da kafa kwamitin da zai haɗa wakilan masu sarrafa shinkafa, manoma da ma’aikatar noma domin tattauna hanyoyin cimma matsaya.
Sai dai wasu daga cikin masu sarrafa shinkafar na ganin cewa duk wata matsaya da kwamitin zai cimma ba za ta yi tasiri sosai ba idan gwamnati ba ta magance matsalar shigo da shinkafa daga ƙasashen waje da sauran matsalolin da ke ƙara kuɗin samarwa ba.
#RicePrice #Shinkafa #Nigeria #RiceProcessors #RIPAN #UmzaRice #Agriculture #FoodSecurity #CostOfLiving #NigerianEconomy #AbubakarKyari #Kano #BBCHausa #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa #NexViewTV

Comments
Post a Comment