Tinubu Ya Lissafo Nasarorin Tattalin Arziki, Ya Ce Najeriya Ta Kai Wani Muhimmin Mataki


 


Tinubu Ya Lissafo Nasarorin Tattalin Arziki, Ya Ce Najeriya Ta Kai Wani Muhimmin Mataki


Umar Nusaiba Ibrahim 


Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana wasu sauye-sauyen tattalin arziki da ya ce Najeriya ta samu tun bayan da gwamnatinsa ta karɓi ragamar mulki, yana mai cewa ƙasar na shiga wani sabon mataki na bunƙasar tattalin arziki.


A cikin jawabin da ya gabatar wa ‘yan Najeriya a ranar samun ‘yancin kai, Tinubu ya ce tattalin arzikin ƙasar ya fara nuna alamun farfaɗowa, inda ya ambaci haɓakar tattalin arziki da ta wuce kashi huɗu cikin ɗari a shekarar 2026, tare da gudummawar ɓangaren man fetur da sauran sassan tattalin arziki.


Shugaban ya kuma ce an samu raguwar satar ɗanyen mai, yayin da hauhawar farashin kayayyaki ta ragu daga matakin da ta kai a baya. Ya ƙara da cewa an sake gina ajiyar kuɗaɗen waje, kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta samu daidaito, sannan Najeriya ta samu sama da dala biliyan shida daga fitar da kayayyakin da ba na man fetur ba a shekarar 2025, wanda ya bayyana a matsayin mafi girma da ƙasar ta taɓa samu.


Tinubu ya ce waɗannan ba maganganun da ba su da tushe ba ne, yana mai cewa ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, ‘yan jarida, ƙungiyoyin sa-kai da cibiyoyin kuɗi na duniya sun lura da sauye-sauyen da ake samu a tattalin arzikin Najeriya. Ya ce ƙasar ta kai wani muhimmin mataki, inda ya bayyana cewa lokacin “maganin gaggawa” na tattalin arziki ya ƙare, kuma an fara kafa tubalin sabon ci gaba.


Ya ce manufar gwamnati a yanzu ita ce mayar da ci gaban tattalin arzikin zuwa abubuwan da ‘yan Najeriya za su iya gani a rayuwarsu, ciki har da sauƙaƙa farashin abinci da sufuri, samar da wutar lantarki mai inganci, samun rance, samar da ayyukan yi da inganta harkokin ilimi. Ya kuma yi alkawarin ƙara tallafa wa noma, bunƙasa masana’antu da inganta hanyoyin sufuri kamar tituna, layin dogo, tashoshin jiragen ruwa da wuraren ajiyar kayayyaki.


Shugaban Ƙasar ya amince cewa har yanzu miliyoyin ‘yan Najeriya na fama da tsadar abinci, kuɗin makaranta, magunguna da sufuri. Sai dai ya ce gwamnati na ƙarfafa shirye-shiryen tallafin jama’a tare da aiwatar da manufofin da za su samar da ci gaba mai ɗorewa. Tinubu ya ce burin gwamnati ba wai kawai rage talauci ba ne, sai dai kawar da shi, yana mai bayyana cewa Najeriya ta wuce matakin gyaran tattalin arziki zuwa wani sabon zamani na wadata da damar samun ci gaba.



#NexViewTV #Tinubu #Nigeria #IndependenceDay #NigeriaAt66 #Economy #TattalinArziki #Arewa #ArewaNews #LabaranArewa #HausaNews #BBCHausa #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa #FreedomRadioKano #DailyTrust #LabaranKasa



Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

KANO BRIDE SENTENCED TO DEATH BY HANGING 9 DAYS AFTER WEDDING