Tsohon Shugaban NPA, Aminu Dabo, Ya Yi Murabus Daga APC
Tsohon Shugaban NPA, Aminu Dabo, Ya Yi Murabus Daga APC
Umar Nusaiba Ibrahim
Tsohon shugaban Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA), Architect Aminu Dabo, ya yi murabus daga kasancewa mamba a jam’iyyar APC, nan take.
Aminu Dabo, wanda ya taɓa zama shugaban ƙungiyar ’yan jam’iyyar APC a Ƙaramar Hukumar Dambatta ta Jihar Kano, ya sanar da murabus ɗin nasa ne a cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 7 ga Oktoba, 2026, wadda ya aikawa shugaban jam’iyyar na mazabar Dambatta Gabas.
A cikin wasiƙar, Dabo ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bayan yin nazari sosai kan wasu dalilai na kansa da kuma shirye-shiryensa na gaba. Ya kuma tabbatar da cewa ya miƙa wasiƙar murabus ɗin ga jami’an jam’iyyar da abin ya shafa domin ɗaukar matakan da suka dace.
Tsohon shugaban na NPA ya gode wa shugabannin APC bisa damar da suka ba shi na yi wa jam’iyyar hidima, da kuma goyon baya da amincewar da suka nuna masa a lokacin da yake cikinta.
Aminu Dabo ya taɓa neman takarar gwamnan Jihar Kano, sannan ya riƙe muƙamin kwamishinan filaye na jihar. Haka kuma, shi ne mamallaki kuma babban jami’in gudanarwa na Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Aminu Dabo da kuma Kwalejin Kimiyyar Jinya ta Aminu Dabo, waɗanda ke Kano.
#AminuDabo #APC #KanoPolitics #Dambatta #NPA #SiyasarKano #SiyasarNajeriya #KanoState #NigeriaPolitics #Resignation #Labarai #BBCHausa #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa #NexViewTV

Comments
Post a Comment